27 Oktoba 2021 - 16:31
​Sudan: An Mayar Da Firaminista Abdallah Hamdok Zuwa Gidansa

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, an mayar da Firayi Ministan kasar Sudan Abdallah Hamdok zuwa gidansa da ke cikin birnin Khartum.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kafin wannan lokacin dai rahotanni daga kasar ta Sudan sun ce sojoji sun yi awon gaba da Hamdok da iyalansa zuwa wani wuri da ba a sani ba, amma daga bisani Abdulfattah Burhan shugaban majalisar gudanarwa ya sanar da cewa, Hamdok yana gidansa, kuma ana ba shi kariyar da ta kamata.

A ranar Litinin da ta gabata ce dai sojojin kasar ta Sudan karkashin jagorancin Burhan suka tarwatsa gwamnatin rikon kwaryar kasar da ke karkashin jagorancin firayi minista Abdallah Hamdok, tare da kame galibin ministocin kasar gami da wasu manyan jami'ai, da suka hada har da gwamnan Khartum.

Yanzu haka dai Burhan bayan rusa majalisar ministoci, ya kuma rusa majalisar gudanarwa wadda yake jagoranta, inda a yanzu sojoji ne karkashin jagorancinsa suke rike da komai a kasar ta Sudan, duk kuwa da cewa ya ce abin da suka yi ba juyin mulki ba ne.

Jama'a dai suna ci gaba da gudanar da zanga-zanga a ko'ina a fadin kasar domin nuna rashin amincewa da wannan matakin na hambarar da gwamnatin rikon kwarya da sojojin suka yi, inda ya zuwa yanzu akalla mutane 7 ne sojojin suka harbe har lahira a yayin zanga-zangar a jiya a birnin Khartum da kuma Ummudrman, yayin da kuma wasu da dama suka jikkata.

Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da Allawadai da wannan juyin mulki na sojojia kasar ta Sudan.

342/